5 Mayu 2025 - 10:23
Source: ABNA24
Aikin Hajji Manhaja Ce Ta Wayewar Musulunci, Kuma Hanya Ce Ta Tabbatar Da Al’umma Daya Dunkulalliya.

Babban Sakatare Janar na Majalisar Ahlul Baiti (AS) ta duniya da yake jaddada fa’idar aikin Hajji da damarmakin da ke cikinsa, ya dauke ta a matsayin dandali ne na tabbatar da al’ummar musulmi, ya kuma yi kira da a zurfafa amfani da wannan aiki na gina wayewa daga manyan mutane, jami’ai, da mahajjata.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa Ahlul Bayt (as) - ABNA - ya habarta cewa: Ayatullah Reza Ramezani Babban Sakatare Janar na Majalisar Ahlul Baiti (AS) ta duniya ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa kan aikin Hajji mai taken: (Muhimmancin Aikin Hajji Wajen Gina Al'ummar Musulmi) da aka gudanar a makon da ya gabata tare da halartar gungun manya manyan malaman makarantun hauza bisa daukar nauyin cibiyar bincike ta aikin hajji da Ziyara a birnin Qum inda ya ce: "Hajji wata dama ce ta musamman da za a yi amfani da ita wajen gina al'ummar musulmi da kuma karfafa su.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da wani hadisi daga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa’alihi Wasallam), ya kira aikin hajji a matsayin wata alama ta alakar da ke tsakanin al'ummar musulmi ta duniya, ya kuma kara da cewa: "Tare da sallah da zakka, aikin hajji yana iya share fagen sadarwa a duniya tsakanin musulmi, da musayar al'adu, da karfafa fahimtar kasancewar al'umma kwara daya".

Ayatullah Ramezani bai dauki aikin Hajji a matsayin ibada kawai ba, sai dai ya gabatar da shi a matsayin wani dandali na tarbiyyar halaye, da karfafa kyawawan dabi'un dan Adam, da fadada al'adun tauhidi, yana mai karawa da cewa: dabi’u irin su hakuri, ikhlasi, sadaukarwa, da amana suna kunshe cikin wannan ibadar.

Yayin da yake jaddada yanayin siyasar aikin Hajji, ya dauki hakan a matsayin wata alama ta hadin kai da karfin siyasa na musulmi yana mai cewa: Aikin Hajji tunatarwa ne na yukunrin tauhidi kamar yunkurin Annabi Ibrahim (AS) da juyin juya halin Manzon Allah (SAW) kuma yana iya karfafa ruhin yaki da zalunci da fasadi.

Babban Sakatare Janar na Majalisar Ahlul Baiti (AS) ta duniya ya dauki aikin Hajji a matsayin dandali mai dacewa wajen hada kai a tsakanin al'ummar musulmi, yana mai karawa da cewa: Tara miliyoyin mutane a Arafat da Mina wata dama ce da ba za ta misaltuwa ta hadin kai, musayar gogayya, da kuma mafarin yunkurin al'umma kwara daya a duniya baki daya.

A yayin da yake ishara da abin da ya shafi tattalin arzikin Hajji, ya ce: “Lokacin da aka saukar da suratu At-Tawbah, wasu sun damu da tabarbarewar tattalin arziki, amma Alkur’ani ya yi alkawarin samun wadata da biyan bukata. A yau, idan aka tafiyar da aikin Hajji yadda ya kamata, zai iya taka rawa a fannin tattalin arziki da samar da karfi cikin ruwan sanyi.

Ayatullah Ramezani ya kara da cewa: Musulunci yana da cikakkiyar manhaja ta gina wayewa, kuma aikin Hajji yana daya daga cikin muhimman abubuwan da suke tabbatar da wannan wayewar. Ba kamar sauran wayewa ba, wayewar Musulunci tana da ikon 'yantar da bil'adama daga rikice-rikice na dabi'a da ruhi.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da hudubar Mina na Imam Husaini (AS) ya ce: “Wannan huduba abin koyi ne na gina al’umma da kuma nuna cewa aikin Hajji wani dandali ne na bayyana manyan al’amurran addini da zamantakewa”.

Yayin da yake sukar yadda makiya suke mayar da hankali kan bambance-bambancen addini, ya ce: “A yau mulkin mallaka maimakon haifar da rarrabuwar kawuna tsakanin ‘yan Shi’a da Sunna, sai ya haifar da rarrabuwar kawuna a cikin mazhabobi. Dole ne mu koma kan ka'idoji na bai daya, mu ci gaba da tattaunawa kan al'adu kan hanyar gina kasa.

Har ila yau Ayatullah Ramezani ya dauki "ka'idar wajibci" a matsayin dabarar huldar kasa da kasa, inda ya kara da cewa: Hatta wadanda ba musulmi ba za a iya gayyatarsu zuwa ga kyawawan dabi'u da tunani nasu, kuma wannan damar tana nan a Musulunci.

Daga karshe ya jaddada cewa: Dole ne a samar da cikakkiyar takarda don gina al’umma ta yadda aikin Hajji da sauran damarmakin kasashen musulmi za su iya taka rawa wajen tabbatar da adalci, wayar da kan jama'a, da hadin kan duniya baki daya.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha